Daga Maryam Muhammad

Hukumar dake yaki da masu yiwa arzikin kasa ta’annati EFCC ta fara binciken wasu kudade da ake zargin ankarkatar dasu kimanin naira biliyan 35 a ma’aikatar tsaro ta kasa.
An rawaito cewar an ware kudaden ne domin siyo kayayyaki ga dakarun sojin kasar nan a aikin da sukeyi na wanzar da zaman lafiya.
A wani rahoto da manema labarai ta bayyana cewar tun a shekarar 2008 akayi awon gaba da wadannan kudaden sannan kuma tace ofishin dake kula da kudaden bashi na kasa ne ya saki wadannan kudaden ga ma’aikatar tsaron kasar nan.
Sannan kuma hukumar ta EFCC ta bayyana sunan tsohon ministan tsaro na kasa Kayode Adetokunbp da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonothan da Mike Oghiadomhe a matsayin wadanda ake zargi akan wadannan kudade.
Hukumar ta EFCC ta bayyana cewar ta kama daractan kamfanin da ma’aikatar tsaron kasar nan ta baiwa kwangilar mai suna Donald Peterson mai shekaru 47.
Hukumar tace a bisa iron bayanan da suka samu daga hannun Peterson tsohon.

Leave a Reply

%d bloggers like this: