Tare da Yahaya Bala Fagge

Wasu da ba’a san ko su wanene ba sun kashe mataimakin Kwamishinan yan sanda na jihar Cross River mai suna ACP Egbe Eko Edo.
Kakakin ƴan sandan jihar Irene Ubo ta tabbatar da faruwar lamarin tace, lamarin ya faru ne a daren jiya Talata.

Sannan ta ce an kasheshi ne lokacin daya je kaiwa yan uwansa ziyara , inda motarsa ta lalace sai ya kira matarsa da taje ta dauke shi, amma kafin zuwanta ne sai aka kai masa harin aka kasheshi har lahira.

ACP Egbe Eko Edum shine shugaban rundunar 73 PMF Squadron dake Mangumeri a jihar Barno.
Ta kara da cewa zasi cigaba da bincike domin ganin an kamo wadanda sukai aika akar.
