Cikin sanarwar da Mallam Abba Anwar babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano ya fitar, sanarwar ta ce Ganduje ya kaɗu matuƙa a bisa harin da aka kaiwa mutanen Ɗanbatta.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalai da al’ummar ƙaramar hukumar Ɗanbatta a bisa hallaka mutane 16 da ƴan bindiga suka yi.

An hallaka mutanen ne a kan hanyar Abuja zuwa Kano.

Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin babban al’amari mai ruɗarwa.

Sannan ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su cigaba da bada gudunmawa wajen gudanar da addu’o’i don samun zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.

Ganduje ya yi addu’ar Allah ya gafarwa waɗanda suka rasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: