Rundunar ƴan sanda a jihar Yobe ta kama wani mutum mai shekaru 38 a duniya bayan yay i wa wata yarinya fyaɗe sannan ya halaka ta.

Mutumin mai suna Sani Sale ana zargin sa da yi wa wata yarinya fyaɗe wanda yay i sanadiyyar rasuwar ta.

Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar Yobe ASP Abdulkarim Dungus y ace lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Fika a jihar.

An aiki yarinyar domin siyar ƙosai a ranar 10 ga watan da muke ciki, kuma ba a sake ganin ta ba sai gawarta aka gani a cikin ɗakin mutumin.

Tuni aka miƙa ƙorafin zuwa babban sashen binciken manyan laifuka a hukumar ƴan sanda don faɗaɗa bincike.

Kakakin ƴan sandan Abdulkarim Dungus ya ƙara da cewar da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotun a bisa laifin da aka same shi ya aikata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: