Shugaban kasa Muhammad Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga rundunar yan sandan Najeriya da iyalan tsohon Sufeto Janar na “yan sandan Mustapha Tafa Balogun bisa rasuwar sa a ranar Alhamis a Jihar Legas.

Mai taimakawa shugaba Buhari na Musamman Femi Adesina shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa.

Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ne a jiya juma a ya ce a lokacin da Tafa Balogun ya ke bakin aiki ya tsaya tsayin daka wajen ganin jami’an “yan sanda sun gudanar da aikin su yadda ya kamata.

Shugaban ya kara da ce marigayin ya baiwa rundunar yan sanda gudummawa yadda ya kama a lokacin aikin sa tare da kara bai wa wasu gwarin gwiwa a cikin aikin.

Tafa Balogun ya rasu yana da shekara 74 bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi a Jhar Lagas.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: