Labarai
Game damu
GAME DAMU:
Kamfanin Mujallar Matashiya yana wallafa MUJALLA a kowane wata, sannan ba shi da alaka da wani ko wata, ko bangaranci na siyasa ko na addini.
Mujallar tana zagaya jihohi 18 na fadin kasar nan, za kuma ku iya tallata hajarku don karin bayani sai a kira 08096399266.
BURINMU:
SAMAR DA AIKIN YI GA MATASA, BUNKASA AIKIN JARIDA CIKIN HARSHEN HAUSA
Labarai
Tinubu Ya Yi Zazzafan Martani Kan Kisan Da Akayiwa Sojoji A Delta
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi martani kan kisan sojoji 16 da aka yi a wani kauye da ke jihar Delta.
Tinubu ya bai wa hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa umarnin zakulo wadanda ke da hannu a kisan tare da hukunta su.
Har ila yau, shugaban ya ba da umarnin makamancin wannan ga hedkwatar tsaron da ke birnin Abuja domin bincike mai tsauri.
Shugaban ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da sanya wa hannu a jiya Lahadi 17 ga watan Maris.
Ya ce kai hari kan jami’an sojoji kamar aiwatar da hari ne kan kasar baki daya inda ya ce ba zai lamunci haka ba a mulkinsa.
Ya kuma tura sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da abokan aikinsu da kuma masoyansu baki daya.
Labarai
Gwamnan Borno Ya Dana Harsashin Gina Asibitin Hakori Da Na Ido
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya aza harsashin gina asibitin ido da hakora a garin Biu, da ke karamar hukumar Biu ta jihar.
Asibitin idon, zai kunshi dakunan tiyata guda biyu, dakunan tuntuba, bangaren gudanarwa, da kuma dakunan maza da mata wadanda ke da gadaje 56 sannan kuma.
Sannn asibitin hakori, za a samar da dukkan kayan aikin da ake bukata don ba da kulawa ga lafiyar hakori.
Zulum, yayin da yake gargadin ‘yan kwangilar da su tabbatar da bin ka’idojin aiki, ya gindaya watanni shida don kammala aikin.
Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta amince da gina wasu asibitocin ido da na hakori guda biyu da za a yi a kudanci da arewacin Borno domin su karfafa na birnin Maiduguri.
Labarai
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Yin Kuskure Wajen Ceto Daliban Da Akayi Garkuwa Da Su A Kaduna-Sheik Ahmed Gumi
Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin yin kuskure wajen ceto daliban makarantar kuriga 287 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne ta cikin wani shiri na gidan Talabijin na Arise TV a birnin tarayya Abuja.
Gumi ya ce kuskure ne yin amfani da karfin iko gurin ceto daliban daga hannun ‘yan bindiga, kamar yadda gwamnati ta bai’wa jami’an tsaro umarnin kubutar da daliban.
Malamin ya kara da cewa bai kamata gwamnatin tarayya ta bai’wa jami’an tsaro umarnin kubutar da daliban ba da karfin ikonta domin hakan zai kasance matsala garesu.
Gumi ya ce yin sulhu da maharan ne kadai zai kawo karshen duk wani ta’addanci da suke aikatawa a Kasar.
Sannan Malamin ya bukaci gwamnatin da ta samar da wani shirin yin yafiya ga maharan domin kawo karshen su a fadin Kasar.
Malamin ya ce bayan yin afuwa ga maharan, a samar da hanyoyin ilmantar da su domin samar musu da kyakkyawar rayuwa.
-
Mu shaƙata1 year ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Labarai1 month ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya5 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida