Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin karbe ikon gudanarwar filin jirgin saman Jihar Gombe.

Gwamnan Jihar Muhammad Inuwa Yahya ne ya bayyana haka a jiya juma’a a fadar shugaban kasa Muhammad Buhari da ke birnin tarayya Abuja a wata ziyara da ya kai masa.

Gwamnan ya ce matakin hakan da aka dauka zai taimaka wajen kara samar da kayan aiki harma da kuɗaɗen gudanarwa da samar da ingantaccen aiki a filin jirgin saman Jihar ta Gombe.

Gwamna Inuwa Yahya ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammad Buhari ne ya bayar da umarnin karbe ikon gudanarwa.

Gwamnan ya bayyana cewa mafi cancanta shi ne filin jirgin Jihar ya koma ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya.

Gwamnan Inuwa ya ce a halin yanzu tuni rundunar sojin saman Najeriya ta fara gina sansanin ta a harabar filin jirgin wanda kuma idan ya koma ga hannun gwamnatin tarayya za a kara samar da kayan aiki.

Kazalika gwamnan ya kara da cewa filayen jirgin sama na cikin jerin ayyuka na musamman da ke karkashin doka.

Sannan ya ce baya ga kara samar da kayan aiki da za a yi za kuma a samar masa da ingantacciyar gudanarwa tare da samun damar sake bunkasa wanda kuma hakan zai tallafa wajen kara habaka fannin kasuwanci sakamakon samar da filin jirgin.

Gwamnan Jihar Gombe ya ce ya je fadar shugaba Buhari ne domin mika godiya bisa nagartattun ayyukan raya Jihar wanda gwamnatin tarayya ta yi.

Gwamna ya bayyana cewa ayyukan da gwamnatin ta yi musu zai bunkasa tattalin arziki tare da samar da ayyukan a Jihar wanda zai dakile yunkurin batagari wanda su ka fara samun gurbin zama a yankin Gandun-Daji Wawa-Zange da ke cikin Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: