Wata kotu da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dage sauraron shari’ar da gwamnatin tarayya ta shigar da kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa ASUU a kan yajin aikin sai babatagani da ta ke ci gaba da yi.

Kotun ta dage sauraron karar ne a yau Litinin tare da sanya ranar 16 ga watan Satumban da mu ke ciki domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Kotun ta bayyana cewa ta dage sauraron shari’ar ne domin gwamnatin ta samu damar mika mata dukkan wasu takardu da su ka dace akan karar da ta shigar gabatan.

Gwamnatin tarayya ta shigar da karar kungiyar ta ASUU gabatan kotun ne a jiya Lahadi domin ta janye daga yajin aikin da ta ke ciki.

Kotun ta bayyana cewa ta dauki matakin hakan ne domin ta gudanar da shari’ar yadda ya kamata.
Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne fiye da watanni shida domin ganin an biya musu bukatunsu.
