Kungiyar kare hakkin fulani makiyaya ta Miyatti Allah ta bayyana cewa a yayin zaben shekarar 2023 mai zuwa za su goyawa jam’iyyar APC ba.

Sakataren kungiyar ta Miyatti Allah Saleh Alhassan ne ya tabbatar da hakan a yayin wata fira da yayi da jaridar Punch a yau Asabar.
Sakataren kungiyar ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wa kungiyar alkawarin magance dukkan matsalolin da ke cikin shirin kula da dabbobi da tare da dawo da hanyoyin kiwo guda 450 a fadin Najeriya.

Saleh Alhassan ya ce an kirkiro shirin shiga tsakani na dabbobi na tsawon shekaru biyu bayan dakatar da shirin da ake yi na karkara.

Sakataren ya kara da cewa nufar gwamnatin tarayya ita ce ta magance rashin jituwa da ke tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar.
Saleh ya ce koda a baya wasu Jihohin kudancin kasar sun bukaci a yi dokar haramta kiwo ko kuma fulanin su sayi filaye domin yin kiwon wanda hakan zai magance rikicin da ke tsakanin su da manoman.
Alhassan ya bayyana cewa matukar Tinubu da Shattima su ka hau kan karagar mulki za su magance masu dukkan muradan su.
Sakataren ya kara da cewa sun amince da zaban jam’iyar APC ne bayan wata wasika da dan takarar jam’iyyar ta APC ya aike musu tare da amincewa da dukkan bukatun kungiyar.