Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya EFCC ta gano kimanin N13bn a matsayin kudin karya da aka biya kamfanoni da sunan tallafin man fetur.

Rahoton Punch ya nuna cewa an biya wadannan makudan kudi ne tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021 a lokacin da gwamnati take daukar nauyin tallafin.

EFCC da take da nauyin yin bincike da hukunta badakalar tallafi mai da gas a Najeriya ta gano N12,998,963,178.29 da aka karkatar wajen biyan kudin bogi.

An yi haka ne a lokacin da ake biyan tallafi tsakanin shekarar 2017 da ta 2021.

A shekarar 2017, jami’an EFCC sun gano N4.7bn, sai N4.29bn a shekarar 2018, N2.41bn a 2019, a shekarar 2020 an bankado N416.51m, sai N1.22bn a shekarar 2021.

Akwai damar da za a sulale da biliyoyi ba tare da an farga ba tun daga hako danyen mai domin ba a san adadin gangunan da ake samu a kullum ba.

Baya ga haka, ‘yan fasa-kauri su na sace arzikin Najeriya daga bututun mai. Ko bayan an tace man fetur, akwai masu sulalewa da shi daga gidajen mai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: