Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar yana da yakinin jam’iyyar za ta kai ga nasara duba da irin fitowar dangon-kwari da magoya suka yi mata a Jihar Kano.

A ranar Talata ce dai Tinubu ya ziyarci Kano don kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa Maso Yamma, gabanin shiga zaben Shugaban Kasa a wata mai kamawa.
Da yake jawabi ranar Laraba a filin wasa na Sani Abacha, Tinubu ya ce, manuniya ta nuna cewa a yakin neman zaben nan, jama’ar Kano sun san abin da ya kamata su zaba.

Ya ce yana da yakinin goyon bayan da Gawuna da Garo ke samu zai kai jam’iyyar APC ga nasarar lashe zaben gwamna har zuwa na Shugaban Kasa.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda mutane suka yi dafifi don nuna goyon bayansu ga takararsa.
Anasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci magoya baya da su kada wa jam’iyyar APC kuri’arsu a babban zaben da ke tafe.
Ganduje ya bai wa Tinubu tabbacin cewar kuri’ar jama’ar Kano ta APC ce duba da yadda mutane ke mararin sake ganin jam’iyyar ta mulke su.
Haka kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bukaci jama’ar yankin Arewa maso Yamma da su sake zabar APC don dorawa daga inda Shugaba Muhammadu Buhari zai tsaya.