Gwamnatin Jihar Edo ta ce mutum 26 ne aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin Lassa.

Kwamishinan Lafiya ta jihar, Farfesa Obehi Akoria ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Laraba a Benin.
Akoria ta ce yawaitar karuwar masu cutar a jihar abun damuwa ne.

Don haka ta bukaci jama’ar jihar da su kiyaye matakan kariya domin kare kansu da kuma ‘yan uwansu daga kamuwa da cutar.

Akoria, ta lissafa alamomin cutar kamar zazzabi, ciwon kai, rashin kuzari, ciwon kirji, ciwon makogwaro, amai da gudawa da zubar jini idan ciwon ya yi tsanani.
Ta gargadi mazauna jihar da su guji kona daji, zubar da shara barkatai da kuma kula da tsaftar jiki.
Ta kuma yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su daina kula da cututtukan da ba su da masaniya a kai.