Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa babban bankin Najeriya CBN bai sanya su daga cikin masu ruwa da tsaki akan sauya fasalin kudaden kasar.

Alhaji Sa’ad ya sanar da hakan ne a yayin wata ziyara da babban jami’in gudanarwa na bankin shiyyar Sokoto Dr Dahiru Usman Hadi da wasu jami’an bankin a ranar Alhamis.

Sarkin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun sanyawa bankin idanu domin ya lalubo hanyoyin da zai yi da mutanen kauyeka da zarar wa’adin da ya sanya ya cika.

Alhaji Sa’ad ya ce tun bayan da bankin ya kuduri aniyar sauya kudin ya kamata ya sanya masu ruwa da tsaki amma yaki sanya su a ciki.

Sarkin ya kara da cewa har kawo yanzu da dama daga cikin mutanen karkara ba su sanya an sanya kudaden ba,wanda hakan zai sanya su ki karbar su idan an ba su.

Kazalika Alhaji Sa’ad III ya bukaci babban bankin na CBN da ya kara yin duba akan wa’adin karbar kudaden,wanda rashin isasshen tsaro ke hana mutanen kauyeka kai kudaden su bankuna domin kaucewa batagari da masu garkuwa.

A yayin jawabin Dr Dahiru ya bayyana cewa sun ziyarci Sarkin ne domin sanar dashi sauya kudaden a hukumance tare da neman shawarwari daga gareshi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: