Wasu ‘yan bindiga a Jihar Kaduna sun yi garkuwa da hakimin Chawai na karamar hukumar Kaure ta Jihar Kaduna Cif Joshua Ahmad.

Shugaban kungiyar ci gaban Chawai CDA Mista Abel Adamu ne sanar da garkuwa da basaraken a ranar Laraba ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun kungiyar Mista Raphael Joshua ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da hakimin ne a daren ranar Talata.

Joshua ya ce masu garkuwar sun je gidan basaraken ne da ke Zambina da misalin karfe 9:30 na dare,inda su ka yi awon gaba dashi.

Shugaban ya bayyana wa al’ummar yankin cewa kawo yanzu su na ci gaba da kokari domin ganin an kubtar da basaraken.

Joshua ya ce bayan faruwar lamarin sun shaidawa jami’an tsaron inda su ka fara aikin ceto basaraken.

Daga bisani shugaban kungiyar ta CDA yayi kira ga gwamnati da ta bai wa hukumomin tsaro umarnin ceto hakimin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: