Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su bashi kwana bakwai domin ya kawo karshen matsalolin da su ka kawo karancin sabbin kudade a ƙasar.

Shugaba Buhari ya tabbatar da hakan ne yayin wata ganawa da yayi da gwamnonin APC a fadar sa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a.

Shugaban ya ce zai koma gurin babban bankin Najeriya na CBN da kamfanin da ke aikin buga kudin da su yanke hukunci kafin cikar wa’adin da ya dauka.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa shugaban ya ga wasu rahotanni da ke nuni da karacin kudi ya janye a harkar kasuwanci harma da talakawa.

Shugaba Buhari ya kara da cewa ragowar kwanaki bakwai daga goma da aka sanya na karewar wa’adin karbar tsofaffin kudin za a yi shine tare da shawo kan matsalar da su ka hana tabbatar da tsarin sabbin kudaden.

Buhari ya ce yana sane da halin matsin da ‘yan Najeriya ke ci na sauyin fasalin kudaden amma za a kawo ƙarshen matsalar ba da jimawa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: