Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da umarni ga shugabannin jami’o’I na ƙasa da su rufe makarantu yayin da ya rage ƙasa da makonni uku a gudanar da babban zaɓe a ƙasar.

Matakin hakan ya biyo bayan hukuncin da aka yanke domin baiw a ɗalibai dammar gudanar da babban zaɓen da ake tunkara.

Hukumar kula da jami’o’I na ƙasa NUC ce ta bayar da umarnin ta hannun mataimakin sakataren zartarwa Dakta Christ Maiyaƙi.

Takardar wadda aka aikewa da shugabannin jami’o’I na ƙasa da sauran hukumomin da ke da alhakin jami’o’in na Najeriya.

An bayar da umarnin rufe makarantun ne daga ranar 22 ga watan Fabrairun da mu ke ciki sannan a buɗe don ci gaba da karatu a ranar Talata 14 ga watan Maris mai kamawa.

Umarnin ya samu sahalewa daga ministan ilimi Malam Adamu Adamu kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A Najeriya a na ci gaba da tunkarar babban zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisar dattawa da wakilai a majalisar wakilai da kuma gwamnoni da ƴan majalisar dokokin jihohi da ake sa ran yi a tsakanin watan Fabrairu da watan Maris.

Leave a Reply

%d bloggers like this: