Rahotanni daga jihar Ondo na nuni da cewar da yawan bankunan ƴan kasuwa a yau Alhamis sun kasance a rufe yayin da abokan cinikayyarsu ke tsaye a kofar nbankunan.

Hakan na zuwa ne bayan da wasu masu zanga-zanga su ka ƙona wani banki da rushe wani a jihar Ogun bayan da ake ci gaba da fuskantar ƙarancin takardun kuɗi.

A na zargin an rufe bankunan ne domin tsoron kai musu hari kamar yadda ya faru a jihar Ogun.

Da yawan bankunan ƴan kasuwa yau sunkasance a rufe  musamman a Akure babban birnin jihar.

Duk da kasancewar bankunan a rufe mutane da dama sun tsaya a bakin bankunan domin tunanin buɗewa don cire kuɗi daga asusun ajiyarsu.

Babban bankin Najeriya CBN ne ya samar da sabuwar dokar sauya fasalin kuɗi tare da sanya wa’adin ranar 10 ga watan da mu ke ciki domin daina karɓar tsofaffin kuɗi da aka sauya.

Ko da yake kotun ƙoli a Najeriya ta dakatar da babban bankin da kuma gwamnatin tarayya daga yunƙurin daina karɓar tsofaffin kuɗin daga hannun jama’a

Leave a Reply

%d bloggers like this: