Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce mutanen dasu ka mutu a sanadin girgizar ƙasa a ƙasashen Syria da Turkiyya sun haura 17,000.

Ƙididdigar da hukumar ta fitar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tono gawarwakin da gini ya rufta musu a sanadin girgizar ƙasa.

Kuma ta ce a halin da ake ciki waɗanda abin ya shafa kuma bas u mutu ba a cikin hatsarin da ka iya fin girgizar  ƙasar.

Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa dubban mutane girgizar ƙasar ta raba da muhallinsu.

Kuma har kawo yanzu mutanen da ibtila’in ya shafa bas u da matsuguni ko wani wuri da za su fake a halin yanzu.

Ƙasashe biyun da abin ya shafa ana tsakanin sanyi da dusar ƙanƙasa kuma a haka  waɗanda abin ya shafa ke kwana a titi babu matsuguni ko wajen fakewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: