Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga duk-kan ‘yan takarkaru da su zama masu mutunta ‘yancin masu zabe tare da karbar sakamako mai kyau ko akasin haka.

Buhari ya bayyana haka ne a jiya Laraba a yayin taron kwamitin zaman lafiya na kasa da ya gudana a birnin Abuja.
Taron wadda aka shirya domin bai wa jam’iyyun siyasa da ‘yan takarkaru damar sanya hannu a yarjejeniyar gudanar da zabe lafiya.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa wanda duk bai yarda da sakamakon zaben ba da ya dauki matakin shari’a.

Shugaban ya ce yana sane da damuwa da ake nunawa kan yadda za’a gudanar da zabe za su kasance bayan bayyana sakamakon zaben.
Shugaba Buhari ya kara da bayyana cewa gwamnatinsa tayi aiki tukuru domin tabbatar da barin tahiri na gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci lumana da kwanciyar hankali.