Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kokarin barin ofishin sa da shi da mataimakinsa Osinbajo, an bukacesu da su bayyana adadin kadarorinsu nan da 2’ranar 29 ga watan Mayu.

Wannan ya shafi dukkan ministoci 44 da gwamanoni masu barin gado a shirin kasar na karbar sabbin masu tafiyar da lamuran al’umma.

Wannan batu na fitowa ne daga bakin Mustapha Musa, mai ba shugaban hukumar kula da da’ar ma’aikata ta CCB shawari kan ayyuka gama-gari.

jaridar Punch ta ruwaito cewa, Musa ya tabbatar da cewa, an kammala shirin ba da fom na bayyana kadarorin ga dukkan manyan jami’an gwamnati da ke shirin tafiya da masu shigowa.

cike wannan fom na kadarori bai tsaya kan su shugaba Buhari ba, ya shafi hadimansa, ‘yan majalisun jiha da na tarayya da ma sanatoci har kan shugabannin kananan hukumomi.

A bangare guda, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da gwamnoni 28 masu shigowa su ma za su cike wannan fom din.

Punch

Leave a Reply

%d bloggers like this: