Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Abba Kabir Yusuf da azarbabi bayan nasarar da ya samu a zabe.

A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sa da zumunta an ji Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana sukar Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan ya zargi Abba Kabir Yusuf da yin kalamai tamkar wanda ya zama Gwamna, ya na mai kara tuna masa bai shiga ofis ba.

Gwamna Ganduje yake cewa su na yi wa Abba addu’ar ya yi mulki da kyau, amma duk da haka za su kalubalanci nasararsa a gaban kotun zabe.

Daily Trust ta ce ana samun sabani tsakanin Gwamna Ganduje da Abba Gida-Gida ne bayan zababen Gwamnan ya rika fitar da wasu sanarwa a matsayin shawarwari.
Da yake jawabi ga ‘yan jarida bayan taron addu’o’i da aka shiryawa Bola Tinubu a gidan gwamnati, Ganduje ya ce Abba ya nuna sam bai dace da mulkin Kano ba.