Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi kira da a tsagaita buɗe wuta a ƙasar Sudan, biyo bayan rikicin da ya ɓarƙe a babban birnin ƙasar Khartoum, a tsakanin sojoji da ƴan tawaye.

Jaridar Punch tace shugaba Buhari ya bayyana cewa rikicin ba abin so bane, a yayin da shugaban miƙa mulki na ƙasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Déby Itno, ya kai masa ziyara ranar Lahadi a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari ya kuma bayyana rikicin wanda ya haifar da asarar rayukan ɗumbin mutane a matsayin abin takaici.

Shugabannin biyu sun yi duba kan lamarin inda suka yi kira ga dukkanin ƙasashen da ke maƙwabtaka da Sudan da kuma ƙasashen duniya da su sanya baki domin ganin ɓangarorin masu faɗa da juna sun zauna a teburin sulhu.

Shugaba Buhari ya yi nuni da cewa abin takaici ne halin da Sudan ta tsinci kanta a ciki, inda ya ƙara da cewa ƙasar ta cancanci samun zaman lafiya duba da halin da ta samu kanta a ciki a baya.

Shugaban ƙasar na Najeriya, ya kuma yabawa shugaban na Chadi bisa ƙoƙarin da yake na ganin abubuwa sun sassauta sannan su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya, inda ya ce masa ya ci gaba da ƙoƙartawa a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: