Hukumar kula da gidan gyaran hali a Najeriya NCS tace aƙalla mutane 3,298 aka yankewa hukuncin kisa daga cikin gidajen ajiya da gyara hali na fadin kasar.

Mai magana da yawun hukumar na ƙasa Abubakar Umar ne ya bayyana haka yau yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Abuja.
Yace adadin mutanen ya ƙaru ne sakamakon ba a saurin zartar da hukuncin kisa bayan yanke hukunci.

Ya ƙara da cewa daga cikin mutanen da aka yankewa hukuncin kisa akwai waɗanda su ka shafe shekaru 15 ba a zartar da hukuncin ba.

Sannan mafi yawa daga cikinsu akwai waɗanda aka samu da aikata kisan kai,fashi da makami, da sauran ta’addanci.
Hukumar ta buƙaci gwamnonin Najeriya dasu gaggauta sanya hannu domin ganin an zartar da hukuncin ga waɗanda su ka aikata laifin.