Kotun sauraron korafin zaɓen shugaban kasa ta sha alwashin yin adalci a shari’ar.

Kotun a zaman da ta fara yau Litinin, ta bukaci lauyoyi su guji yin kalamai na hargitsa mutane.

Jagoran da zai shugabanci shari’ar Mai shari’a Haruna Tsammani ya gabatar da jawabin a zaman kotun na yau.

Sannan ya buƙaci lauyoyin da su bai wa lotun haɗin kai domin kammala shari’ar cikin nasara.

Rahotanni sun ce an jibge jami’an tsaro a harabar kotun gabanin fara zaman a yau.

Jam’iyyu da dama ne su ka shigar da korafinsu dmagane da nasarar da Bola Ahmed Tinubu na jamiyyar APC ya samu a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: