Ministan Ilimi a Najeriya Malam Adamu Adamu ya zargi ’yan Arewacin Najeriya da zama musabbabin yaduwar jahilci a yankunan Arewa.

Ministan ya ce duk da cewa ’yan Arewa na bugun kirji da addinin Musulunci wanda ke karfafa neman ilimi, amma kuma su ke yi wa harkar neman ilimi manakisa.
Ya ce, idan ba haka ba, jami’o’i biyu na farko amma kuma wasu a Arewa na fakewa da Musulunci suna hana mata fita neman ilimi.

Ministan ya yi wannan furuci ne a taron kaddamar da manhajar karatun jami’o’i da wani littafi a kansa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta gudanar a Abuja.

Ya jinjina wa NUC bisa kokarinta na kafa sabbin jami’o’i a Najeriya, musamman yadda a baya-bayan nan da akasarin sabbin jami’o’i da hukumar ta ba wa lasisi a yankin Arewa suke.
A ranar Litinin Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da ba da lasisi ga wasu sabbin jami’o masu zaman kansu guda 37 kuma yawancinsu a Arewaci suke.
Adamu ya ce an kaddamar da sabuwar manhajar karatun jami’o’in ne domin tabbatar da ilimin jami’o’i a Najeriya ya dace da zamani.
Don haka ya yi kira da a yi duk mai yiwuwa wajen sama musu wadatattun kayan aiki domin cimma wannan kudiri.