Kotun surron ƙorfi a kan zaɓen shugban Najeiya ta yi watsi da buƙatar jam’iyyar PDP na watsa yadda shari’ar ke gudana kai tsye a kafafen watsa labarai.

Manyan ƴan takarar shugaban ƙasa biyu na jam’iyyun LP da kuma PDP sun bukaci a watsa yadda shjari’ar ke gudana kai tsaye.

Sai dai kotun ta ƙi amincewa da batun a kan cewar babu wata doka a Najerita ta da ba ta damar watsa zaman shari’a kai tsaye a gidan talabiji.

Bisa dogaro da hujjar ne ya sanyta kotun ta ƙi amincewa da buƙatar hakan.

Sai dai jam’iyyun sun buƙaci a nuna yadda zaman kotun ke wakana ganin yadda zaman kotun ke wakana ganin yadda mutane ke nuna sha;awar ganin yadda ake shari’ar.

Kotun ta fara sauraron ƙorafi a kan zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanara  ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar da mu ke ciki.

Bayan fara karɓar ƙorafin kotun ta sha alwashin yin adalci a shari’ar da za ta gabatar a tsakanin masu ƙorafi a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: