Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane uku a gurin hakar ma’adinai da ke kusa da Tanjol a cikin yankin Jol da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Sakataren yada labaran kungiyar matasan Berom ne ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma’a a garin Jos.
Sakataren ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, inda ya ce harin yayi sanadiyyar jikkata mutane biyu.

Tengwog ya kara da cewa ba wannan ne karo na farko ba da ‘yan bindigan su ka taba kai hari yankin.

Sakataren yayi kira ga gwamnatin Jihar da hukumomin tsaro da su kara jajircewa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma musamman na yankunan karkara.
A yayin da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan Jihar bai samu damar daga kiran wayar da aka yi masa ba.