Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nuna rashin jin dadinsa dangane da hallaka manoma takwas da mayakan ISWAP suka yi a cikin ƙaramar hukumar Mafa ta jihar.

Zulum ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai garin na Mafa domin jajantawa ‘yan uwa da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Babagana ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta haɗa hannu da jami’an tsaro a Jihar domin a kara tura jami’an soji domin su bai’wa gonakin da manoman kariya.

Zulum ya kara da cewa Gwamnatin jihar za ta kira taron gaggawa na majalisar tsaro domin samar da hanyoyin wadata manoma da isasshen tsaro.

Gwamnan ya ce za a kafa wata tawaga ta musamman wacce za ta haɗa da jami’an tsaron soji da na sakai da mafarauta da sauran jami’an tsaro domin kare manoman.

Zulum ya bayyana cewa matsalar rashin abinci za ta fi matsalar Boko Haram zama babban rikici a Jihar, inda ya yi nuni da cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da mutane sun samu damar zuwa gonakinsu

Leave a Reply

%d bloggers like this: