Akalla mahajjata shida ne su ka rasa ratukansu a Kasar Saudiyya sakamakon bugun zuciya.

Shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da aikin hajjin bana Dr Usman Galadima ne ya tabbatar da BBC faruwar Lamarin.

Galadima ya bayyana cewa mutanen da su ka rasa rayukansu biyu sun fito daga Jihar Osun sauran kuma sun fito ne daga Jihohin Kaduna da Filato.

Dr Usman ya ce kawo yanzu maniyyata 15,860 ne suka yi jinya sakamakon cututtuka daban-daban.

Ya Kara da cewa daga cikin cutukan da maniyyatan suka yi sun hada da mura gyambon ciki hawan jini da kuma cizon sauro.

Kazalika Dr Usman ya ce sama da mahajjata 100 ne aka kaisu asibitoci a kasar ta Saudiyya.

Sannan ya ce akwai wasu alhazan Najeriya 30 da aka tabbatar da cewa suna da matsalar tabin hankali, inda aka mikasu ga asibitocin Kasar ta Saudiyya,amma kawo yanzu su na cikin koshin lafiya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: