Al’ummar Hausawa da ke cikin karamar hukumar Takum ta Jihar Taraba sun zargi ‘yan kabilar Kuteb da hallaka musu mutane 32 a Jihar.

Mai magana da yawun al’ummar Hausawa a yankin Alhaji Sani Abdullahi shine ya bayyana haka a ranar a garin Jalingo da ke Jihar.

A yayin jawabinsa Alhaji Sani ya bukaci da mahukunta a Jihar su hukunta ‘yan kabilar ta Kuteb da suka kashe Hausawan.

A yayin mayar da martanin sa Shugaban kabilar ta Kuteb Emmanuel Ukwen ya ce zargin da kabilar Hausawa su ke yi musu na kisan mutanensu bashi da tushe balle makama.

Sannan Emmanuel ya zargi kabilar Hausawa da hada kai da makiyaya gurin kai hare-hare kan ‘yan kabilar ta Kuteb.

Ba tun yanzu ba Jihar Taraba ta ke fama da rikice-rikicen kabilanci wanda hakan ke sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin mutane a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: