Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki a birnin tarayya Abuja da kewaye AEDC ya bayyana cewa zai yi karin kudin wutar lantarki sakamakon canjin kudin kasar waje.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa kamfanin shine mai bai’wa birnin tarayya Abuja da Jihohin Neja Kogi da kuma Nasarawa.
A wani sako da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi ya bayyana cewa karin farashin ya zama dole sakamakon hawa da sauka da Naira take yi a kasuwar canji.

Kamfanin ya ce daga ranar 1 ga watan Yuli 2023 za a samu karin kudin wutar lantarki sakamakon tangal-tangal a kasuwar canji ke yi,wanda hakan yayi tasiri a kan farashin akan kudin wutar.

Karin kudin wutar ya samo nasaba ne da sabon tsarin canjin kudin kasar waje da babban bankin Kasa CBN ya fito da shi.