Babban bankin Duniya ya amince da bukatar gwamnatin tarayya na karbo bashin dala miliyan 500 domin taimakawa Najeriya a shirin tallafawa mata.

Bankin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar,inda ya ce ya amince da bashin ne domin tallafawa mata a Najeriya wanda tun da fari aka amince da shi tun a ranar 27 ga watan Janairun 2018 da ta gaba da kudi dala miliyan 100.
Jaridar Punch ta rawaito cewa sabon bashin shine bashi na biyu da bankin na duniya ke amincewa da shi karkashin sabuwar gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.

Sanarwar da bankin ya fitar ya bayyana cewa zai bai’wa Najeriya bashin ne a shirin tallafawa mata na NFWP-SU,sannan kuma zai tallafawa gwamnatin tarayya wajen zuba hannun jari a shirinta na inganta rayuwar matan Najeriya.

Bankin ya kara da cewa shirin na NFWP-SU zai taimaka wajen samar da zaunannan tattalin arziki mai dorewa, wanda hakan zai kawo karshen matsalar rashin daidaito tsakanin jinsi samar da ilmi Lafiya da kuma abinci mai gina jiki ga lafiyar iyali.
Bankin ya kuma bukaci gwamnatin ta Tinubu da ta samar da hanyoyin magance matsalolin da ke hana mata karfin tattalin arziki da kuma kawo musu cikas ga ci gaban tattalin arzikin su.