Rundunar Sojin Najeriya sun kai sumame wani gida da ake zargi ana amfani da shi wajen kyankyasar jarirai tare da safarar mutane a Jihar Adamawa.

Kwamandan runduna ta 23 da ke garin Yola Birgediya Janar Mohammad Gambo ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a hedkwatar hukumar a ranar Litinin.
Janar Gambo ya ce a yayin samamen da su ka kai sun samu nasarar kama mutum bakwai a gidan.

Birgediya Muhammad ya kara da cewa jami’an sun gano gidan ne lokacin da su ke gudanar da wani sintiri na musamman a kan iyakar Najeriya da Kamaru,a bayan samun bayanan sirri da su ka yi akan gidan.

Mohammad ya kara da cewa a lokacin da jami’an suka isa gidan sun samu ’yan mata 17 masu shekara 19 zuwa 21 wadanda suka kasance a sansanin na tsawon shekara 2 zuwa uku ba tare da sanin iyayensu ba.
Daga karshe Janar Muhammad ya jinjinawa jami’annasu akan gano matattarar batagarin, inda ya ce hakan babbar nasara ce ga aikin dakile safarar jarirai da ‘yan mata.