Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya daga ziyara ta musamman da ya tafi kasar Birtaniya.

Shugaban zai dawo ne a yau Talata domin gudanar da bikin babbar sallah da za ayi a gobe Laraba.

Shugaban zai dawo ne bayan shafe kwanaki a Kasar Faransa da Birtaniya.

Wasu na kusa da fadar shugaban sun bayyana cewa bayan dawowar shugaban zai gudanar da bikin sallah ne a Jihar Legas wadda ta kasance sallar shi ta farko akan karagal mulki.

Makusantan sun kara da cewa akwai yiwuwar shugaban zai halarci filin idin na Obalende da ke barikin Dodan a Legas,wanda a baya ya kasance fadar shugaban Kasa.

Sannan sun ce bayan halartar sallar idin da shugaban zai yi ba zai dawo fadarsa ba sai ranar Litinin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: