Mashawarci ga shugaban kasar Nigeriya akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya ce za su kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Ribadu ya bayyana hakan ne cikin jawabin sa na kama aiki a ranar Litinin inda ya lashi takobin kawo karshen tsaron a Nigeria.

Ya kara cewa wannan aikin ne da za’a yi wa ‘yan Nijeriya kuma manufar ita ce cigaba da aikin da aka riga aka soma ya kuma bada tabbatar da samar da hadin kan kasar.

Bola Tunibu ne dai ya nada Nuhu Ribadu a matsayin mai bashi shawara akan harka tsaro a ranar 19 ga watan Yuni 2023 sannan aka daga likkafarsa daga baya .

Leave a Reply

%d bloggers like this: