Hukumomi a Saudiyya sun bayyana cewa za su sauya wa alhazan Najeriya 10,000 mazauni a Mina sakamakon ƙarancin hemomin da suke fuskanta.

Mai magana da yawun hukumar ta NAHCON Musa Ubandawaki ne ya tabbatar da haka a ranar Talata ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ubadawaki ya ce biyo bayan ƙarancin hemomi da abinci da alhazan Najeriya su kai koke za a sauya musu hemomin.

Kakakin ya kara da cewa koda a ranar Litinin sai a karkashin gada wasu alhazan Najeriya suka rika ringa fakewa sakamakon zafin rana da aka yi.

Musa ya ce jami’in Saudiyya mai kula da jin dadin alhazan Najeriya ne ya nemi gafararsu kan halin matsin da Alhazan suka shiga.
Sanann jami’in ya ce za su dauki matakin kwashe Alhazai 10,000 daga cikinsu zuwa hemomin alhazan Turkiyya waɗanda babu kowa a ciki.