A jiya Talata ne aka gudanar da janaizar wani mahauci da aka yi masa ikirarin cewa ya batanci ga Annabi Mahammadu (SAW) a jihar Sokwato.

Wanda lamarin ya faru a gabansa ya bayyana cewa wanda aka kashe bai zagi Annabi ba.
Ya ce hasali Wanda aka hallaka mai suna Usman Buda gyara ya yiwa mai neman bara yayin da yake bara.

Jaridar Daily trust ta ruwaito yadda hawaye ya kwaranya wajen janaizar marigayin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wani mai bara ne yake neman taimako da cewa abashi sadaka saboda Annabi sai Usman da aka kashe ya ke cewa mai barar ba a bayar da sadaka saboda Annabi sai don Allah.
Anan ne fa wani ya ce ana bayar da sadaka don Annabi, sai aka fara musu..
wani ya ce ana neman taimako wajen Allah da Annabi da kuma DanFodio sai Usman ya ce babu kyau haka, nan fa wani ya ce ya zagi Annabi Kuma jininsa ya hallatta.
Jama a suka dakko dutsina suna fara jifansa da kuma yankansa da wuka wadanda suka yi wunkurin cetonsa aka yi musu rauni kafin jami’an tsaro su je aka kashe shi.
Shi ma wani shaida Mai suna Nuhu Bala ya ce ko kadan Usman bai yi batanci ga fiyayyen hallatta ba (SAW).
Sannan ya kasance mahadacin alqur’ani amma wasu da ko fatiha ba su iya ba sun kashe shi a ranar Lahadi karshen mako.
Malam Lukuwa ne ya jagoranci sallar janaizar Usman Buda a babban masallacin juma a na mabera a jihar Sakkwato.
Sannan malam musa Yusuf Asadus Sunnah ya ja hankalin alumma da su daina saurin daukar mataki daga ance wani yayi batanci ga addini su haushi da duka har kisa domin za ta iya kasancewa bai tabbata ba.
Ya kara da cewa daukar doka a hannu jama a ba daidai ba ne abar hukuma ta yi aikinta a cewar shehin malamin