Hukumar NERC ta kasa, ta na jiran amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin a iya bada sanarwar canjin farashin sayen kudin wutar lantarki.

A rahoton jaridar Vanguard aka fahimci sai Bola Ahmed Tinubu ya bada dama ga NERC mai kula da harkokin wutar lantarki, sannan farashi zai iya canzawa.

Sau biyu ake duba farashin sayen wuta a kowace shekara, wajibi ne shugaban Najeriya ya amince tukunna MYTO zai sauka ko kuwa ya karu.

A wannan karo, ana sa ran Mai girma shugaban kasa ya yi na’am da tashin farashin a dalilin karyewar da Naira ta yi bayan an fito da sabon tsarin kudi.

Wata majiya ta shaidawa jaridar a ranar Laraba cewa an karkare aiki a kan farashin da za a fito da shi, abin da ya rage shi ne yin zama da shugaban kasa.

Zuwa ranar Juma’ar nan za a iya sanin ko daga ranar 1 ga watan Yuli za a canza farashi ko kuwa sai an shiga watan Agusta kamar yadda wasu ke fada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: