Gwamnatin Najeriya ta ce ta shigar da nakasassu 500 cikin shirin inshorar lafiya na kasa (NHIS), domin inganta hanyoyin samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.

Babban sakataren ma’aikatar jin kai da ci gaban jama’a, Dakta Sani Gwarzo, ne ya bayyana hakan a wani taron ba da katin cin gajiyar shirin na inshorar lafiya ga waɗanda suka amfana a birnin tarayya Abuja.

Gwarzo ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya jagoranci jami’an ma’aikatar lafiya zuwa fadar sarkin Karo Majiji kuma shugaban masu buƙata ta musamman a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa hukumar kulla da masu buƙata ta musamman ta ƙasa (NCPWD) ce ta dauki nauyin Shirin.

Ya cigaba da bayana cewa an dauki matakin ne domin rage wahalhalun da mutane masu nakasa ke fuskanta wajen samun ayyukan kula da lafiya.

Ya ce gwamnati ta fara aiwatar da shirin ne a babban birnin tarayya kuma ana sa ran za a faɗaɗa shi zuwa jihohi 36 na fadin Najeriya

Leave a Reply

%d bloggers like this: