Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya naɗa tsohon Minista a ma’aikatar noma da raya karkara, Malam Bukar Tijjani a matsayin Sakataren Gwamnati.

A cikin wata Sanarwa da kakakin gwamnan Malam Isah Gusau ya fitar, Sanarwar ta ce Gwamnan Zulum ya yi la’akari ne da ƙwarewar da Bukar Tijjani ya nuna lokacin da ya yi minista daga Watan Yulin shekara ta 2011 zuwa Satumba na shekara ta 2013 da

kuma muƙamin da ya riƙe na Mataimakin babban Darakta na Hukumar Abinci da Harkokin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Malam Bukar Tijjani ya kuma riƙe shugabancin shirin samar da abinci na ƙasa da kuma shirin bunƙasa noman rani na Bankin Duniya a Najeriya wanda aka fi sani da Shirin Noman Rani na Fadama.

Tsohon ministan mai shekaru 62 ɗan asalin ƙaramar hukumar Dikwa ne amma haifaffen garin Damasak dake Arewacin jihar Borno.

Ya yi digirin farko a Amurka a shekarar 1984 sannan ya yi digirinsa na biyu a Ingila a shekarar 1989 duk a fannin noma.

Sanarwar ta ce, a matsayin Gwamna Zulum na farfesa a fannin noman rani ya naɗa tsohon ministan ne a matsayin Sakataren Gwamnati domin taimakawa wurin bunƙasa noma da wadatar da jihar Borno da cikakken abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: