Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta ayyana tafiya yajin aiki na kwanaki biyu kan cire tallafin mai.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau.
Kungiyar ta ce za ta shiga yajin aikin gargadi ne a ranakun Talata da Laraba mai zuwa.

NLC ta kara da cewa za su shiga yajin aikin ne ganin yadda ‘yan Kasar suke ci gaba da fuskantar halin kunci da talauci da kuma wahalhalun rayuwa.

Shugaban Kungiyar na Kasa Joe Ajaero ya tabbatar da hakan a yau Juma’a a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Ajaero ya ce sun dauki matakin hakan ne a yayin wani zama da suka yi da mambobin kungiyar a ranar Alhamis.
Shugaban ya kuma zargi gwamnatin Tarayya da yin watsi da alkawuran da ta daukar musu a yayin ganawar da su ka yi kwanakin baya.
Idan ba a manta ba a watan Agustan da ya gabata sai da kungiyar ta kwadago ta gudanar da zanga-zanga akan halin matsin da ‘yan kasar ke fuskanta bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a Kasar.