Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ‘yan bindiga da sauran wasu masu aikata ta’addanci na shirin samar da wasu dabarun aikata ta’addanci a Kasar.

Babban hafsan sojin Kasa Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana haka a hedkwatar hukumar da ke birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.
Lagbaja ya ce ‘yan bindigar da ke aikata ta’addanci a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Kasar ne suke yunkurin samar da dabarun aikata ta’addaci tare da kai hare-hare kan mutanen yankunan.

Janar Toreed ya kara da cewa ‘yan bindigar sun fara amfani da abubuwan fashewa na IEDs wajen aikata ta’addanci.

Babban hafson ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin sakataren sashen yaki da ta’addanci na majalisar ɗinkin duniya, Vladimir Voronkov.
Kazalika ya ce jami’ansu ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kawo karshen batagarin da suka addabi Kasar.
Sannan ya ce rundunar ta shirya tsaf domin ta hada kai da kungiyar domin dawo da zaman lafiya a fadin Kasar.
Kuma ya nemi goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya kan shirin sauya tunanin tubabbun ‘yan ta’addan da suka tuba.
Anasa bangaren mai taimakawa babban sakataren Dinkin duniya Vladimir Voronkov ya bayyana cewa ma’aikatarsa za ta taimakawa Najeriya wajen binciko masu laifi tare da gurfanar dasu a gaban Kotu.
