Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ba za a ci gaba da tashi da saukar jiragen kasar Dubai ba a kasar.

Ministan sufurin jiragen sama ba kasa Najeriya Fetos Keyemo ya bayyana haka ga manema labarai a wani taro da aka gudanar game da tashin jirage a Abuja.
Da yake bayani Festos ya ce har yanzu tsakanin Najeriya da kasar Dubai hadaddiyar Daular Larabawa ba a cimma yarjejeniya ba.

Ya ci gaba da akwai abubuwan da ya kamata a yi dayawa kafin tashin jiragi a Najeriya.

A ranar Litinin din da ta gabata ne shugaban kasa Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya gana da takwaransa na kasar Dubai wato Sheik Mohamed Abu Zayed game da yarjejeniyar tashin jirgin kasar Dubai da Najeriya.
Sai dai an bayyana cewa an cimma wannan yarjejeniyar amma ministan sufurin jiragin ya ce ba haka abin yake ba ana bukatar abubuwa da dama sannan a fara aikin tashin.
Yarjejeniyar tashin jirgin na Najeriya izuwa kasar Dubai akalla a watan Augusta shekarar da ta gabata ne Kuma har yanzu ba a shigar kasar ta Dubai.