Gwamnatin jihar Filato ta ce mutane 22 ne su ka mutu sannan wasu 132 ne su ka jikkata a ginin da ya ruftawa dalibai a jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai a jihar Musa Ashoms ne ya bayyana jaka a wata sanarwa da ya fitar daren jiya Juma’a.

Ya ce an ceto mutane 154 sannan an tabbatar da mutuwar 22.

Dalibai da malaman da su ka jikkata kuwa tuni su ke karbar kulawa daga likitoci a asibitoci daban-daban na jihar.

Ya ce makarantar na da dalibai 400 bangaren da ginin ya rufta kuwa akwai dalibai 200 a ciki.

Ya ce gwamnatin jihar tuni ta bai wa kowanne asibiti umarnin bayar da kulawa ga wadanda lamarin ya shafa ba tare da tsayawa kididdiga ko tantace abinda za a kashe ba.

Ginin dai ya ruftawa daliban yayin da su ke aji a jiya Juma’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: