Rundunar ya sanda a Jihar Anambra ta kama mutane 200 da ta ke zargi da aikata laifuka daban-daban.

Sannan yan sandan sun kwato makamai daga ciki akwai bindigu kirar AK47 da wasu bindigu kananan kira gida.

Kwamishinan yan sanda a jihar Nnaghe Itam ne ya baayyana haka yayin taron manema labarai da ya gudana a Awka babban birnin jihar jiya Juma’a.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai masu garkuwa da mutane, ƴan fashi da makami, da masu satar motoci.

Ya ce an kama masu laifukan ne cikin watanni biyu.

Ak kwato bindigu daban-daban guda 33 da harsashi guda 1,644 sai ababen hawa na motoci da babura da aka kubutar.

Kwamishina ya buƙaci yan jarida da su kasance masu tuntubar sashen hulda da jama’a na rundunar dangane da kowanne abu da su ka gani a kafofin sadarwar zamani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: