Babbar kotun jihar Kano ta haramtawa Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan Gaya, Karaye, Bichi da Rano amsa kansu a matsayin sarakunan Kano

Kotun ƙarƙashin mai shari’a Jusctice Amina Aliyu ta haramta haakan ne a zamanta na yau bayan da gwamnatin jihar Kano da majalisar dokoki ta jihar da shugaban majalisar da ma kwamishinan shari’a su ka shigar da kara a gabanta tun a watan Maris.

Kotun kuma ta umarci sarakunan da su mayar da dukkanin kaya mallakin gwamnatin jihar Kano

Kafin zaman kotun na yau, lauyoyin waɗanda gwamnatin ke ƙara sun bukaci kotun ta dakatar da shari’ar ganin yadda su ka daukaka kara

Sai dai alkaliyar kotun ta ki amincewa da bukatarsu ganin cewar ba ta samu umarni daga kotun daukaka kara ba.

Haka zalika, sun mika rokon soke sabuwar dokar da majalisar dokoki ta jihar Kano ta shigar amma kotun ta ki aminta, a cewar kotun ba a gabatar mata da gamsassun hujjojin da za ta ƙi aminta da sabuwar dokar majalisar ba.

A zaman da kotun ta yi ranar 4 ga watan Yulin da mu ke ciki ne dai lauyoyin da ke kare Alhaji Aminu Ado Bayero a gaban kotun su ka janye daga kare shi a shari’ar.

Gwamnatin jihar Kano ce dai ta shigar daa kara a gaban kotun ta na mai rokon kotun ta hana Alhaji Aminu Ado Bayero, da sarakunan Gaya Karaye Bichi da Rano amsa kansu a matsayin sarakunan Kano.

Tirkatirkar dai ta fara ne tun baya daa majalisar dokoki ta jihar Kano ta soke dokar karin masarautu tare da dawo a tsohuwar dokar da ta dawo da Malam Muhammadu Sanusi ll a matsayin sarkin Kano.

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: