Gamayyar dattawa a Katsina sun soki ministan tsaro a Najeriya Muhammad Badaru Abubakar da karamin ministan tsaro Bello Matawalle Kan yawaitar hare-haren yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Sakataren kungiyar Alhaji Ali Muhammad ne ya bayyana haka a madadin sauran mambobin, ya ce ministocin biyu wadanda su ka fito daga yankin arewa maso yammacin kasar babu wani abin a zo a gani da su ka yi a kan matsalar.
Ya zargesu da kin zuwa don jajantawa mutane bisa halin da su ke ciki na hare-haren da su ka fuskanta daga yna bindiga.

Wanda hatta shugaban kasa maa bai yi wannan yunkurin ba.

Kungiyaar ta shawarci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya dauki sabbin matakai don kawo karshen matsalar da ta mamaye yankunan.
Ya ce sun yi korafi sau da dama sai dai babu wata hobbasa da gwamnaatin ke yi a kai.
Ya ce duk da darurwan mutanen da aka lashe a Jihar babu minista ko dhugaban kasa da ya jajantawa mutane a kai.
Ya kara da cewa matukar da gaske shugaban kasa yake a kan kawo karshen yan bindiga to ya zama wajibi ya sauke shugabannin tsaro domin sun gaza a bangaren
Haka zalika kungiya ta nuna damuwarta dangane da tsadar kaayan abinci da ake fuskanta, wanda ya ce ya kamataa shugaban kasa ya bude kunnensa don sauraren koken jama’a tare da daukar hanyaar kawo gayara a bangaren.