Akalla shaguns 15 ne su ka kone a wata gobara da ta faru a jihar Ogun.

Lamarin ya faru a kasuwar Oba Lipede da ke Kuto a karamar hukumar Abeokuta ta jihar.
Rahotanni sun ce an yi asarar miliyoyin dukiya a sanadin tashin gobarar.

Haka zalika akwai wani mutum guda da ya jikkata

Gobarar ta fara ne a daren Asabar wayewar safiyar jiya Lahadi.
Mafi yawan kayan da aka yi asara sun hada da Shinkafa, ayaha da wasu kayan abinci.
Haka kuma akwai tsanar kudi da su ka kone na yan kasuwar.
Shugaban kasuwar Tejumade Bakre ya ce an sacewa mutane kayayyaki bayan faruwar gobarar.
Sai dai jami’an tsaro sun isa wajen don kubutar da kayan.
Hukumar kashe gobara a jihar ta ce wutar lantarki da gas wanda ya haddasa gobarar a kasuwar.