Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a sabuwar dokar kafa masarautu uku masu daraja ta biyu.

Majalisar dokokin jihar Kano ce ta gabatarwa da gwamnan sabuwar dokar wadda za a kirkiri masarautu a Gaya, Karaye, da Rano.

Masarautun dai za su zauna ne kaarkashin sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll tare da karbar umarni daga wajensa.

Haka zalika gwamnan zai nada tare da bayar da sanda ga sarakuna ukun da majalisar dokokin jihar ta kirkira.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da wata babbar kotu a Kani ta yanke hukuncin a jiya wanda ta ke nuni da kin amincewa da dokar da majalisa ta yi na rushe masarautu hudu tare da dawo da Malam Muhammadu Sanusi ll

Haka kuma kotun ta hana sarakuna huɗu da Alhaji Aminu Ado Bayero amsa sunan sarakuna a Kano.

Sai dai matakin nada sabbin marasautu masu daraja ta biyu ana ganin zai bar baya da kura, yayin da ake ganin tsugune ba ta kare ba ganin yadda batun ke gaban kotuna daban-daban a cewar masana shari’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: