Fiye da mutane 150 aka sace bayan halaka wasu huɗu a ƙaramar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Daga cikin waɗanda aka sace har da jarirai biyu yan ƙasa da shekara guda.

Maharan sun shiga kauyen Dan Isa da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara kamar yadda wani da aka sace matarsa da dan sa ya tabbatar.

Ya ce yan bindigan sun shafe awanni shida a cikin kauyen wanda su ka shida a karfe 03:00pm na ranar Lahadi.

Haka kuma sun shiga ƙauyen haye kan babura wanda kowannensu ke dauke da mutane uku.

Da zuwansu su ka fara harbin iska lamarin da ya sanya mutane su ka fara gudun ceton rai.

Jami’an yan sanda ba su ce komai a dangane da harin ba

Wannan dai na zuwa ne bayan da yan bindiga su ka saki mutane 46 da su ka sace a kauyen Dogon Kade baya da su ka bukaci biyan naira miliyan 21.

Leave a Reply

%d bloggers like this: